Alfijr ta rawaito Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka, ICPC, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Hassan Ahmad da makudan kudi Naira miliyan 2 a cikin jaka yayin da yake tuka wata mota kirar Hilux daga jihar Bauchi. zuwa makwabciyar jihar Gombe.
ICPC ta yi zargin cewa kudin na nufin a kai wa wani dan siyasa da ba a bayyana sunansa ba a Gombe don yiwuwar siyan kuri’u.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, wacce ta wallafa a shafinta na Twitter da aka tabbatar, ta ce jami’an runduna ta 33 na Artillery Brigade Operation Safe Conduct da aka tura karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi ne suka kama Ahmad.
Daga nan ne sojojin suka mika wanda ake zargin ga ICPC a Bauchi.
Wanda ake zargin, a cewar hukumar, ya mallaki sabbin takardun kudi N900,000 da kuma tsofaffin takardun kudi naira miliyan 1.1.
Hukumar ta kara da cewa ana kai wadannan kudade ne a wata bakar mota kirar Hilux mai lamba JMA 85 AZ.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇