Rundunar Ƴan Sandan Kano Sun Kama Ƴan Daba 83 Yayin Bukukuwan Sallah

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama ‘yan daba 83 a lokutan bukukuwan karamar Sallah da aka yi.

Kakakin rundunar ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce kamen masu laifin ya taimaka wajen gudanar da bukukuwan Sallar lafiya a jihar.

“An kama ‘yan daba 83 daga tsakanin ranar Juma’a 21 ga Afrilu da ta kama Sallah zuwa Talata 25 ga Afrilu a lokutan Hawan Daushe da Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi a fadin masarautu biyar na jihar,” in ji sanarwar.

Hakazalika “An kama masu laifin da mugayen makamai da kwayoyi da kuma kayayyakin sata a hannunsu.”

Sanarwar ta ce an yi wannan aiki ne karkashin umarnin da Babban Sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali Baba ya bayar na tabbatar da samar da tsaro a lokutan hidimomin sallah.

Kiyawa ya kara da cewa mun godewa sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula da sarakuna da ‘yan sa kai da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen dakile aikata miyagun laifuka a lokutan hidimar.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaron al’ummar Jihar Kano, tare da gargadin masu aikata laifi da kuma jan hankalin mutane da su ci gaba da yi wa jihar addu’a.

A karshe ya bayyana cewar, yanzu haka ana fadada binciken masu laifin, domin gurfanar da su gaban kotu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *