Alfijr ta rawaito Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wasu ƙwayoyi masu yawa a jihohin ƙasar huɗu.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu aka kuma wallafa.
Ya bayyana cewar hukumar ta ce ta kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 3,975kgs da ƙwayar tramadol 58,200.
Hakazalika a samamen da jami’an hukumar suka kai jihohin Kaduna da Kano da Imo da kuma jihar Legas, ta ce ta kama mutum 11 da take zargi da hannu.
Hukumar ta ce mutanen na amfani da dabaru da dama wajen shigar da ƙwaya zuwa Najeriya tare da yunƙurin fitar da ita zuwa ƙasashen waje irin su Birtaniya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yaba wa jami’an hukumar a waɗannan jihohi bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen wannan kame.
Haka kuma ya yi kira ga sauran jami’an hukumar a faɗin ƙasar da su tashi tseye domin kawar da harƙallar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇