
Alfijr ta rawaito Gwamna Matawalle yace ya fadi zaɓe ne saboda wannan Ƙara da suka shigar da gwamnatin tarayya, inda Uba Sani yasha da ƙyar yayin da Gawunan Ganduje yasha kayi shima
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwar sa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Najeriya CBN yayi.

Gwamnan ya zargi cewar, wasu fulogai a cikin gwamnatin tarayya da yin yaƙi dashi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba.
Idan za’a iya tunawa dai, Matawalle yayi takara ne a jam’iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ta kayar dashi.

Idan zaku iya tunawa Gwamna Matawalle yace ya fadi zaɓe ne saboda wannan Ƙara da suka shigar da gwamnatin tarayya, inda Uba Sani yasha da ƙyar yayin da Gawunan Ganduje yasha kayi shima
Shari’ar da suka shigar haɗe da wasu gwamnoni, sunyi nasara akan gwamnatin tarayya tun kafin zaɓe

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Need Curren news update