Iran ta yi watsi da wa’adin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya mata, na cimma yarjejeniya ko kuma buɗe mashigin Hormuz ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Tun da fari, Mista Trump ɗin ya yi barazanar saukar wa ƙasar abin da ya kira “ruwan wuta” idan har ba ta amince da yarjejeniya cikin kwanaki biyu ba.
A wata sanarwa, shugaban rundunar ƙoli ta sojin Iran, Janar Ali Abdollahi, ya bayyana Trump ɗin a matsayin “firgici da wauta”.
Ya kuma gargaɗin cewa abun da Trump ɗin ke fatan saukar wa Iran a ƙarshe zai ƙare ne a kan Amurka”
Ya ƙara da cewa idan Amurka ta kai hari kan muhimman kayayyakin more rayuwa na Iran, to Tehran za ta kai hari kan wuraren da sojojin Amurka da Isra’ila ke amfani da su “ba tare da wani shamaki ba”
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t