Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya tura shi wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin yin alƙawarin komawa jam’iyyar APC idan aka samu nasara a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ta shekarar 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce Kwankwaso ya buƙace shi da ya je wajen Tinubu, har ma ya yi rantsuwa da Alƙur’ani kan alƙawarin komawa APC.
A cewarsa, bayan zaɓen shekarar 2023, sun tattauna da Tinubu, inda suka cimma matsayar cewa idan Shugaban Ƙasa bai tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ba, za su koma APC bayan samun nasara.
Abba Kabir ya ce Kwankwaso ne ya tura shi domin tabbatar da wannan yarjejeniya, tare da ba shi shawarar cewa idan hakan ya zama dole, ya ɗauki Alƙur’ani ya rantse cewa za su koma APC idan Allah Ya ba su nasara.
Gwamnan ya ƙara da cewa daga baya Kwankwaso ya yi watsi da yarjejeniyar da suka cimma, duk da cewa, a cewarsa, shi ne ya jagoranci shirin da kuma ɗaukar alƙawarin.
Ya kuma bayyana cewa Kwankwaso ya sha ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, tare da tura tawaga domin tattauna batun komawarsu jam’iyyar APC.
Dangane da komawarsa APC, Abba Kabir ya ce ba ya kallon matakin a matsayin butulci ga Kwankwaso, domin a ganinsa, shi ya cika alƙawarin da aka ɗauka, yayin da tsohon jagoransa ya kasa yin hakan.
Gwamnan ya koma jam’iyyar APC a hukumance a ranar 26 ga Janairun 2026, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar 23 ga Janairu. Matakin ya haifar da gagarumin sauyi a siyasar Kano tare da ƙara tsananta saɓanin siyasa tsakaninsa da Kwankwaso.
A cikin tattaunawar, Abba Kabir ya kuma yi ƙarin bayani kan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da matarsa, Zainab Musa Kwankwaso, da kuma ƙalubalen tsaro da jihar Kano ke fuskanta.
ALFIJIR LABARAI — Accurate • Timely • Trusted.
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
