Akwai yiwuwar a yi wa kyaftin din Portugal, Cristiano kuma dan wasan gaban Al-Nassr Cristiano Ronaldo za ayi masa bulala 99 idan ya koma Iran.
Alfijir Labarai ta rawaito Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya gana da mai goyon bayansa, mai zane Fatima yayin da yake tafiya zuwa Iran domin buga gasar cin kofin nahiyar Asiya da kungiyar Persepolis a watan Satumba.
Ronaldo ya runguma tare da sumbatar yarinyar, lamarin da ake ganin babban cin zarafi ne ga dokar Iran a wajen aurenta.
Sai dai har yanzu ba a tuhumi tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid a hukumance ba.
A halin yanzu Ronaldo yana tare da tawagar kasar Portugal yayin da suke shirin karawa da Slovakia da Bosnia & Herzegovina a wasannin neman cancantar shiga gasar EURO a ranakun Juma’a da Litinin.



Rouydad24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo