
Alfijr ta rawaito Wata kotun yankin Jos ta tsakiya da ke zamanta a Kasuwan Nama 1 a ranar Alhamis, ta raba auren shekara 8 da aka yi tsakanin wata Samira Makama da mijinta, Muhammed Musa, saboda rashin iya biyan bukatunsa.
Kwamitin alkalan da suka hada da Malam Sadiq Adam da Mr Hyacinth Dolnanan a wajen amincewa da bukatar da Makama ya gabatar, sun ce duk kokarin sasanta bangarorin ya ci tura.
Alkalan sun umarci mai kara da wanda ake kara da su bi hanyarsu ta daban.
Kotun, ta umurci wanda ake kara da cewa ya rika kula da ‘ya’yansa duk wata tare da biyan kudin makarantarsu.
Tun da farko dai matar ta roki kotu da ta raba auren nasu, inda ta ce mijin nata da ta yi aure shekaru 8 da suka gabata ya kasa kula da ita da ‘ya’yansu biyu.
Ta shaida wa kotun cewa tun farko mijin nata ya sake ta har sau biyu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan kuma ya yanke zumunci da ita.
Samira ta bayyana cewa ta je kotu ne domin neman a raba aurenta da wanda ake kara
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ