Kishi! Wata Sabuwa, Wani Ɗalibi Ya Kashe Kansa

Alfijr ta rawaito Wani ɗailibin ajin ƙarshe a kwalejin fasaha ta tarayya ta Oko da ke jihar Anambra ya kashe kansa saboda budurwarsa ta juya masa baya.

Wata majiya ta bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa ɗalibin ya ɗauki matakin ne bayan da budurwar da ya ke matuƙar so ta ce masa ya je ya nemi wata budurwar.

Rahotonni sun ce ɗalibin, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, na koyon sanin makamar aiki gabanin kammala karatun na sa.

Majiyar ta ce marigayin ɗalibi ne mai ƙwazo da hazaƙa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *