A ƙoƙarin samar da ruwan sha mai tsafta, da araha, Korbit Table Water, shine babban kamfanin samar da ruwa, mai inganci tare da tsaftataccen mazubi masu tsafta.
Alfijir labarai ta ruwaito shugaban kamfanin Alhaji Garba Ahmed Ibrahim ya ce, kamfanin yana amfani da sabuwar fasahar zamani don tabbatar da cewa ruwansu yana fuskantar tsauraran matakai na amfani da Reverse Osmosis (R.O.) da Ozone Generator wa’yanda suke kalkale ruwan sha.
Ya kara da bayyana cewar Kwalbar Dispenser din Korbit yana da famfon ruwa na lantarki mai caji ta atomatik, sabanin wanda ake da su a baya.
Tare da wannan samfurin, abokan cinikin mu za su iya jin daɗin shan ruwa mai tsafta cikin yanayi mai sauki.
Kamfanin ya saukaka wa abokan cinikinsa samun kwalaben Korbit ta hanyar samar da shi a rumfunan Dillalanmu manya da kantunan da ke fadin kasar nan, wadanda suka hada da Sahad Store, Best Medix, Sadaraki, DanAljanna, Jujin Labbu, da sauransu.
Garba ya kara da cewa ga masu sha awar cinikayya da mu, tsofaffi da kuma sabbin customers, suna iya ziyartar waɗannan wurare da aka lissafa a sama ko tuntuɓar kamfanin kai tsaye ta lambobin wayar:
08123172526, 08166665444, ko 08096233122.
Korbit yana alfahari da sadaukar da kai ga inganci da aminci.
Ɗaya daga cikin mahimman fa’idodin zabar ruwan tebur na Korbit shine, kokarinsa na kiyaye ɗanɗano tayin amfani da kyakkyawan mazubi domin samar da tsaftataccen ruwan sha ga kowa da kowa.







Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj