Jirgin sama ɗauke da alhazai 442 ya yi saukar gagagawa bayan samun sako cewa an dasa bom a cikinsa

FB IMG 1750177656488

Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su da suka kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasar Indonesiya.

A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya.

’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa.

Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi.

Ta bayyana cewa bayan kwashe mutanen,  ’yan sanda sun fara aikin bincike domin gano bom ɗin da kuma lalata shi.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *