Jihohin Arewa 4, Da Ke Kan Gaba Da Ke Fama Da Matsanancin Talauci

Alfijr ta rawaito Jihohin Arewa shida ne ke da ‘yan Najeriya miliyan 42.75 da ke fama da talauci, kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Jihohin-Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto, Jigawa, da Bauchi sun zama jahohi shida da suka fi fama da talauci tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.

Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa, Kano, Kaduna, Katsina, da Sokoto suna da miliyan 31.28. na ’yan Najeriya masu fama da talauci masu dimbin yawa.

Wannan yana kunshe ne a cikin
Kididdigar Talauci na Muti-Dimensional Poverty Index da NBS ta buga ranar Alhamis.

Ana auna ma’aunin ta hanyar amfani da lafiya, ilimi da yanayin rayuwar ‘yan Najeriya.

Hukumar ta NBS ta ce adadin fatara ya tashi da kashi 63 cikin 100 zuwa miliyan 133.

Arewa tana da miliyan 86 daga cikin talakawa 133 na Najeriya, a cewar NBS. “Sokoto na cikin jihohin da suka fi fama da talauci, kuma tana da matalauta miliyan 5.8 tsakanin al’umma miliyan 6.4. Tana fuskantar ƙalubale masu mahimmanci.

Sai dai a Kano mutane miliyan 10.5 na fama da talauci; duk da cewa jihar Kano na fama da talauci ya ragu, wanda ya shafi kashi 66.3 na al’ummar jihar maimakon Sokoto kashi 90.5 cikin 100,” in ji NBS.

Al’ummar Kano bisa ga NBS miliyan 15.9 ne.

A cewar NBS, kashi 78 cikin 100 na mutanen da ke zaune a Zamfara na fama da talauci, inda ta kara da cewa kudin da ake kashewa wajen magance radadin talauci a jihar zai bukaci a ware kasafin kudi mai yawa.

NBS ta ce, “Za a yi tsada a rage radadin talauci a Zamfara, inda tsananin talauci ya yi yawa, kashi 42 cikin 100 saboda kowane talaka a Zamfara yana fuskantar rashi a lokaci guda.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

One Reply to “Jihohin Arewa 4, Da Ke Kan Gaba Da Ke Fama Da Matsanancin Talauci”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *