Iran ta kaddamar da sabon hari da makamai masu linzami a kan Isra’ila, wanda ta sa masa suna “Honest Promise

IMG 105748 14625 1749895087768

A safiyar ranar Asabar, din yau ne Iran ta kaddamar da wani sabon hari da makamai masu linzami a kan Isra’ila, wanda ta lakaba masa suna “Honest Promise 3”.

Wannan harin ya biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a baya wanda ya yi sanadin mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran da fararen hula a wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni daga kafofin yada labarai na Cikin gida kamar Almayadeen Al-arabiya sun bayyana cewa harin ya kunshi jefa gagaruman makamai masu linzami da kuma wasu jiragen yaki marasa matuki (drones) zuwa yankunan Isra’ila, da nufin ɗaukar fansa kan abin da Iran ta kira “kisan kai ba tare da wani dalili ba da Isra’ila ta aikata.”

Ma’aikatar tsaron Iran ta ce wannan hari wani ɓangare ne na jerin martanin diflomasiyya da soja da kasar ke dauka don kare martabarta da tsaron iyakokinta.

Wannan shi ne karo na uku cikin jerin hare-haren da Iran ke ɗaukar nauyin su, wadanda aka sanya wa suna “Honest Promise”, domin mayar da martani ga hare-haren da suka shafi sojojinta ko abokan ƙawancenta.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *