Alfijr ta rawaito a kalla mutane 21 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan da wata motar bas ta fada cikin magudanar ruwa a Arewacin Kasar Masar ranar Asabar.
A cewar Al Jazeera, Sherif Makeen, jami’in ma’aikatar lafiya a Masar, ya ce yara uku na daga cikin wadanda suka mutu.
An ce mutane 35 ne suka shiga cikin motar a lokacin da ta fada cikin magudanar ruwa.
Ko da yake babu wani tabbaci a hukumance kan hakikanin abin da ya haddasa hadarin, an ce lamarin na da nasaba da wata matsala ta sitiyari.
Motar bas din da ta fada mashigin Mansuriya da ke Aga, wani gari da ke cikin gundumar Dakahlia a Masar, yanzu an samu nasarar gano su.
Wannan ci gaban na zuwa ne makonni bayan mutuwar mutane takwas bayan wani hatsari da ya rutsa da wata motar safa a hanyar Sukhna-Galala a Masar.
Hadarin, wanda ya faru a watan Satumbar 2022, ya yi sanadin jikkata wasu sama da 30.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ