Ibtila’i! Jirgin Saman Sojin Najeriya ya yi Hatsari a Jihar Kaduna

Screenshot 20240701 102548 Chrome

Daga Aminu Bala Madobi

Wani karamin jirgin saman rundunar sojan saman Najeriya ya yi hatsari da safiyar ranar Litinin din nan a kauyen Tami dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Shaidar gani da ido ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safe abinda ya haifar da firgici ga al’ummar yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin na kan hanyar sa ta aiki yayin da ya fuskanci matsala wacce ta kai ga faduwarsa.

Sai dai bayanai sun nuna cewa matukin jirgin ya samu tsira.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *