
Alfijr ta rawaito Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, Buba Marwa, ya amince da kara wa’adin daukar ma’aikata da mako guda.
Wannan na zuwa ne domin baiwa masu nema damar samun cin gajiyar ƙarin kwanakin don kammala aikin.
Mista Marwa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ya fitar. Femi Babafemi, ranar Alhamis a Abuja.
An bude tashar ta yanar gizo ne a ranar Lahadi, 12 ga Maris, kuma an shirya rufe ta ne a ranar Asabar, 8 ga Afrilu.
Sai dai shugaban hukumar ta NDLEA, ya ce da karin mako guda, tashar za ta ci gaba da kasancewa a bude har tsakar dare ranar Litinin, Afrilu. 17.
“Wannan zai baiwa masu neman wanda har yanzu basu kammala aikinsu ba da kuma masu sha’awar shiga amma duk da haka su yi amfani da karin kwanakin su cika fom dinsu a portal.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ