Hukumar ICPC ta gayyaci Dangote bisa korafin da ya shigar kan tsohon shugaban NMDPRA

FB IMG 1766393458371

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC ta gayyaci Aliko Dangote da ya bayyana a gaban kwamitin  masu bincike a ranar Litinin a Abuja, dangane da wani korafi da ya rubuta.

Dangote ya shigar da koke ne kan Ahmed Farouk, tsohon Darakta janar na hukumar Kula da harkokin man fetur na  (NMDPRA), bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wata majiya  a hukumar, wadda ta tabbatar da hakan a ranar Lahadi a Abuja, ta ce ICPC ta kafa wani kwamitin kwararrun masu bincike domin gudanar da binciken.

A cewar majiyar, Shugaban ICPC, Dakta Musa Aliyu (SAN), ya umarci tawagar da ta mai da hankali kan koken Dangote.

Ana sa ran Dangote zai halarta da kansa ko kuma ya tura lauyansa, Ogwu Onoja (SAN), tare da hujjojinsa, yayin da binciken koken zai fara a hukumance.

Dangote ya zargi Farouk da cin hanci da almubazzaranci da kudaden gwamnati, ciki har da kashe miliyoyin daloli wajen biyan karatun ’ya’yansa hudu a makarantu masu tsada kuma na musamman a ƙasar Switzerland.

Har ila yau, ya yi zargin cewa Farouk ya raunana tace man fetur a cikin gida ta hanyar hada kai da ’yan kasuwar ƙasashen waje da masu shigo da man fetur, ta ci gaba da bayar da lasisin shigo da man.

ICPC ta bukaci Dangote da ya mika dukkan hujjojinsa ga hukumar yaƙi da cin hanci, tare da tabbatar da cewa za ta yi adalci ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *