Hukumar Hisbah Ta Damƙe Mawaƙi Al’Ameen G fresh A Kano

Alfijr ta rawaito Mawaƙi G Fresh Ya gurfanane bisa zargin wasa da Sallah wanda sashin Kai Sumame na Hukumar ta Hisbah suka nemo shi, suka kuma mikawa Sashin Da’awa na hukumar karkashin jagorancin Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah Ustaz Hussaini Ahmad Chediyyar Kuda bisa Umarnin babban Kwamandan Dr. Ibn Sina.

Bayan kamashin, Malaman hukumar sunyi masa nasiha da nusantar dashi hadarin wasa da addini.

Sun Kuma Shawarce shi da ya koma makaranta dan gyaran addininsa.

Ba tare da bata lokaci ba Mawaƙin Al’amin G fresh yayi alkawarin gyara al’amuran sa, kuma ya rattaba hannu a takarda kan yarjejeniya idan ya sake Hukumar Hisbah zata dauki mataki na gaba a kansa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *