Alfijr ta rawaito Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta fara gwanjon motoci 435 da ta kama a jihar Lagos kamar yadda dokar da ta kafa EFCC ta shekarar 2004 da dokar Yin kwangila ta shekarar 2007 da kuma dokar Ƙwace dukiyar da aka mallaka ta haramtacciyar hanya ta shekarar 2022 suka tanada.
Hukumar ta EFCC tana aikin ne kafada da kafada da hukumar lura da yadda ake kashe kudaden gwamnati (BPP) domin tabbatar da bin doka wajen wannan aikin.
Shi dai wannan aikin da aka shirya gudanar da shi a dukkanin shiyyoyin hukumar dake ƙasar nan, za’a fara da duba motocin ranar Talata 6 ga watan Disamba, 2022 a ikko daga bisani kuma a fara gwanjon ranar Laraba zuwa Alhamis 7 da 8 ga watan Disamba 2022. cikin Dokokin Hukumar, ya fara ne a ranar Talata, 6 ga Disamba, 2022 a Lagos
Ana kuma samun kayayyakin a wurare hudu: 40, Bourdillon Road, Ikoyi, Legas; 15A Awolowo Road, Ikoyi, Lagos; 14 Cameroon Road, Ikoyi Lagos da CHU Obalende, Ikoyi, Legas.
Da yake jawabi yayin bude taron a jiya, sakataren hukumar ta EFCC kuma shugaban kwamitin da ke kula da kadarorin da za’a yi gwanjon nasu ADC, Dr.George Ekpungu, ya ce: “Aikin wanda shi ne na farko a jerin shirin yin gwanjon kadarorin da hukumar ta ƙwato a sassan shiyya da hedikwatar hukumar na kasa gaba-daya. Shi dai wannan shiri ana aiwatar da shi ne bisa Dokar EFCC (Establishment), 2004, Public Procurement Act, 2007 da Proceed of Crimes (Recovery and Management) Act, 2022.
“Haka kuma ana gudanar da shi tare da hadin gwiwa da hukumar lura da yadda ake bada kwangila (BPP) don tabbatar da bin doka da kaidojin gwamnatii” .
A lokacin da yake karbar kwararru akan harkar gwanjo ya nuna jin dadinsa ga hadin kai da hukumar ke samu daga hukumomin gwamnati musamman sojojin Najeriya da aka gayyace su domin samar da isasshen tsaro a wajen wannan babban aiki.
Ekpungu ya kuma yi kira ga jama’a da suka halarci wurin gwanjon da su saurara da kyau ga masu yin gwanjo tare da bin duk ka’idojin da aka gindaya.
Kamfanoni Masana akan gwanjo guda tara aka gayyato don duba motocin dake jibge a ofishin shiyya na hukumar dake gidan mai lamba 14 Cameron Road, Ikoyi, Legas, sune: Rihanna Auction Limited; Kamyus Consult Limited; Areogun Resources Limited; BIS N JEG;Integrated Services Nig.Ltd;Mau & Sons Ltd.; Langar Aghaji & Co.; Fagobe Ltd da Musa Kira and Co.
Motocin da za’a yi gwanjon din an karkasa su rukuni-rukuni domin baiwa kwararrun damar duba su kafin kuma a zaɓi wanda ya samu nasarar zama mai gwanjon da zai jagoranci aikin gaba-daya.
Hukumar ta EFCC dai zata duba kwarewa da cancanta wajen zabar wanda zai jagoranci gwanjo.
Manufar hakan shine bada dama ga duk mai bukata ya nuna sha’awarsa ga duk motar da yake bukata.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇