An karrama Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, da lambar yabo ta ƙasa da ƙasa bisa kyakkyawan shugabanci da ayyukan ci gaban al’umma da gwamnatinsa ke aiwatarwa, tsawon shekaru 7.
An ba shi lambar yabon ne a birnin Landan, karkashin shirin African Business Leadership Awards (ABLA), inda aka yabawa nasarorin da gwamnatin Yobe ta samu a fannonin lafiya, ilimi da noma.





Gwamna Buni ya sadaukar da wannan nasara ga al’ummar Jihar Yobe, yana mai cewa hakan zai ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da yi wa jama’a aiki da gaskiya da rikon amana.
Wanene Mai Mala Buni Gwamnan Jihar Yobe Ne?

An haifi Mai Mala Buni a ranar 19 ga watan Nuwamba, shekarar 1967 a garin Buni Yadi da ke karamar hukumar Gujba a Jihar Yobe. Tun yana karami ya fara karatun Al-Qur’ani kamar yadda al’adar Hausawa da Kanuri ta tanada a Arewa.
Mai Mala yayi karatun firamare a makarantar Buni Gari Central Primary School, inda ya samu shaidar kammala firamare a shekarar 1979. Daga nan ya wuce Government Secondary School Goniri, inda ya kammala karatunsa na sakandare a shekarar 1985.
Duk da kasancewarsa cikin harkokin siyasa tun yana matashi, bai bar neman ilimi ba. Ya samu digirin farko a fannin International Relations daga Espan Formation University. Sannan ya kara samun digirin digirgir daga Leeds Beckett University a fannin International Relations.
Siyasa
Kafin fitowarsa a siyasar kasa, Mai Mala Buni ya fara siyasa ne tun daga matakin karamar hukuma, a shekarar 1991 ya zama kansila mai wakiltar mazabarsa, kuma daga baya aka zabe shi Kakakin Majalisar Karamar Hukumar Gujba.
Wannan mataki ya kasance tamkar makarantar koyon shugabanci ne a gare shi, domin ya fara fahimtar yadda gwamnati da siyasa ke aiki tun daga tushe.
Bayan haka, ya rike mukamai daban-daban a siyasa da gwamnati, ciki har da:
1. Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin siyasa,
2. Mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa,
3. da kuma jagoranci a jam’iyyun siyasa daban-daban kafin kafuwar APC.
Lokacin da aka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013, Mai Mala Buni ya kasance daya daga cikin wadanda suka taka rawa wajen gina jam’iyyar daga tushe.
Da farko ya zama shugaban APC a Jihar Yobe, kafin daga baya a shekarar 2014 aka zabe shi Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa.
A matsayinsa na Sakataren APC na kasa, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben shekarar 2015, wanda ya kai ga nasarar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mutane da dama a APC suna yabawa Mai Mala Buni saboda: natsuwa, iya sasanta rikice-rikice, da kuma biyayya ga tsarin jam’iyya.
Zamansa Gwamnan Jihar Yobe
A shekarar 2019, Mai Mala Buni ya tsaya takarar gwamnan Jihar Yobe karkashin jam’iyyar APC, kuma ya samu nasara. Daga nan ne ya zama gwamna na hudu na Jihar Yobe tun bayan dawowar dimokuradiyya.
Tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan:
1. Gina tituna,
2. Bunkasa ilimi,
3. Kiwon lafiya,
4. Noma,
5. da kuma dawo da yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa.
A lokacin mulkinsa an gudanar da manyan ayyukan kamar haka:-
1. Gyaran makarantu da Gina Sabi ,
2. Gina asibitoci,
3. Samar da hanyoyin ruwa,
4. Da kuma tallafawa matasa da manoma.
Mutane da dama a Yobe suna yabawa gwamnatinsa saboda salon mulkinsa na, sauraron jama’a, aiki cikin natsuwa, da kuma mayar da hankali kan ci gaba maimakon yawan surutu na siyasa.
A tattaunawar Jaridar Alfijir Labarai da wani na kusa da gwamnan jihar Yobe Alhaji Lawan Damaturu wanda aka fi sani da (Lawaita Madugu) Shugaban kamfanin ALW Construction Nigeria limited ya bayyana cewar,
Abin da ya fi daukar hankalin mutane game da Mai Mala Buni shi ne: Tsoron Allah Tawali’u, hakuri, Iya mu’amala da jama’a, da kuma gujewa siyasar hayaniya.
Lawaita ya sake cewa ko da yana rike da manyan mukamai a kasa, an san shi da saukin kai da kusanci da jama’a. Yawanci yana fifita aiki cikin shiru ba tare da neman yabon jama’a ba.
Mutane da dama a Yobe suna kallonsa a matsayin shugaba mai:
1. Hangen nesa,
2. kishin jihar Yobe,
3. da kuma son hada kan jama’a.
Kasuwanci Da Gudunmawa
Baya ga siyasa, Mai Mala Buni ya taba gudanar da harkokin kasuwanci tun yana matashi, musamman a fannoni kamar: Noma, Sufuri, Gine-gine, da harkokin man fetur.
Wannan ya taimaka masa wajen fahimtar tattalin arziki da yadda za a samar da ayyukan yi ga jama’a.
Karramawa da Lambobin Yabo
Saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen shugabanci da ci gaban kasa.
Gwamnatin tarayya ta ba shi lambar yabo ta ƙasa ta: Commander of the Order of the Niger (CON).
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t