Gwamna Fubara ya buƙaci magoya bayansa su yi godiya ga Shugaba Tinubu

FB IMG 1748686612048

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu ya samar da maslaha a jiharsa.

Fubara ya bayyana haka ne a wani taro da magoya bayansa suka shirya a Fatakwal, inda ya ce matakin na Tinubu ya taimaka sosai, wanda a cewarsa hakan ne ya har ya zama zai cigaba da kasancewa a matsayin gwamna.

Tashar Channels ta ruwaito shi yana kira ga magoya bayansa da su yi godiya ga shugaban, inda ya ƙara da cewa ba don Tinubu ya shiga tsakani ba, da rikicin ya wuce abin da ake tunani.

Fubara ya kuma yi godiya ga magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya bisa nuna masa ƙauna, “ina godiya sosai da addu’o’inku.”

“Babu dalilin da za a ce ba za mu zauna lafiya da ogana ba,” in ji shi a lokacin da yake bayyana alaƙarsa da Ministan Abuja. Nyesom Wike.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ga Masu Bada Talla Zasu Iya kiran+2348032077835

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *