Ganduje ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa ga dalilin

FB IMG 1751042625748

A cikin wani mataki da ya ba da mamaki, Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Ganduje, tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya bayyana dalilin neman lafiya a matsayin abin da ya sa ya yanke shawarar sauka daga kujerar, yana mai cewa yana bukatar mayar da hankali kan lafiyarsa.

Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito cewa duk da cewa takardae murabus din na sa ta danganta saukarsa da batun lafiya, majiyoyi da ke da masaniya da al’amarin sun nuna cewa akwai yiwuwar rikici na siyasa a cikin jam’iyyar ya taka rawa wajen yanke shawarar da ya dauka.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, ana danganta saukarsa da zarge-zargen almundahana da suka shafi harkar kuɗi, inda wasu mambobin jam’iyyar suka bayyana rashin jin daɗinsu kan “yawan bukatun kuɗi fiye da kima” da ofishinsa ke kakaba.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835i

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *