Farashin litar man fetur ya tashi a sassa daban-daban na Najeriya a safiyar yau Talata.
Alfijir Labarai ta rawaito masu ababen hawa a arewaci da kudancin ƙasar duk sun bayyana yadda farashin ya tashi daga yadda aka saba gani.
Haka nan an ga dogayen layukan ababen hawa a Abuja, babban birnin ƙasar.
A Abuja, babban birnin ƙasar wani gidan mai na kamfanin NNPC tsakiyar birnin ya ƙara farashin litar man zuwa naira 617 haka nan ma wasu gidajen man na ƴan kasuwa.
Hakan ya yi sama idan aka kwatanta da naira 539 da ake sayarwa a baya.
Wani mazaunin Jos, babban birnin jihar Filato ya ce ya sayi litar mai ɗaya a kan naira 617 a safiyar Talata, sama da naira 537 da aka saba saye gabanin hakan.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Allah kayi mana inuwa da inuwarka a ranar da babu wata inuwa sai inuwar ka