Alfijr ta rawaito Hukumar EFCC a Jihar Lagos ta soma gudanar da bincike kan Oluwadarasimi Omoseyin kan zargin lalata darajar sabbin kuɗin Najeriya.

Omoseyin Jarumar fim ce kuma mai sana’ar gyaran jiki, an kama ta ne tun a ranar Laraba bayan wasu bayanan sirri da hukumomin yaƙi da cin hanci suka samu a kanta.
Sumamen nasu sun sami nasarar kama matashiyar ƴar shekara 31, bayan ganin wani bidiyo yana yawo a shafukan sada zumunta wanda aka ga tana liƙa kuɗi kuma tana tattake su a wajen wani biki.
EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da jarumar gaban kotu da zarar an kammala bincike, domin ta girbi abinda ta shuka.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇