EFCC ta Ƙwato Biliyan 30 Daga Cikin kuɗaɗen da ma’aikatar jin kai ta wawashe

FB IMG 1704870772714

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga cikin N37,170, 855,753.44 da ake zargin an wawure a ma’aikatar jin kai a karkashin tsohuwar ministar, Sadiya Umar-Farouk.

Alfijir labarai ta rawaito majiyoyi a hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wadanda suka zanta da wakilim Jaridar Funch a ranar Juma’a, sun ce hukumar ta kuma gano sama da Naira miliyan 500 daga badakalar da aka yi da magajiyar Sadiya Umar-Farouk, Betta Edu, wadda shugaba Bola Tinubu ya dakatar a kwanakin baya.

Idan zaku tuna a cikin watan Disamba an fitar da Biliyan 37 daga asusun gwamnati tare da aika zuwa wasu asusun banki 38 da ke cikin wasu manyan bankunan kasuwanci guda biyar na mallakar ko kuma alaka da wani dan kwangila, James Okwete.

An tattaro cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumar EFCC ta kwato N30bn biyo bayan sanya hannun jari a asusun bankin Sadiya Umar-Farouq da Okwete, wadanda har yanzu jami’an hukumar da ke binciken cin hanci da rashawa ke ci gaba da binciken su.

Har ila yau hukumar na ci gaba da garkame Betta Edu dangane da badakalar Naira biliyan 17, yayin da kuma Ko’odineta na shirin zuba jari na kasa, Halima Shehu, kuma har yanzu ana yi Masara tambayoyi kan badakalar N44bn.

Majiyar EFCC ta bayyana cewa, “Hukumar a yanzu ta kwato sama da N30bn daga cikin N37.1bn da aka karkata akalarta da tsohuwar ministar, Sadiya Umar-Farouq. Mun samu nasarar kwato kudaden ne bayan da muka sanya lamuni a asusun ajiyar tsohon ministar kuma dan kwangilar Mista Okwete, wanda ake alakanta shi da badakalar da ake bincike. Duka ministan da dan kwangilar har yanzu masu binciken mu suna gasa su a kullum.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *