FITOWA TA 3
A yau, ana yawan amfani da kalmomin Fim, Wasan Kwaikwayo da Shirin Talabijin. Wasu lokuta ma ana ɗaukar su a matsayin abu guda.
Amma shin da gaske duk abu ɗaya ne?
A wannan fitowa, za mu yi bayani kan ma’anar kowannensu, yadda ake samar da su da kuma bambancin da ke tsakaninsu.
1. MENENE FILM?
Fim (Film) wani aikin gani da sauti ne da ake samarwa ta hanyar ɗaukar hotuna masu motsi, tare da sauti ko ba tare da sauti ba, domin gabatar da labari, bayani ko wani lamari ga masu kallo.
Ana iya shirya fim ta hanyar amfani da jarumai, hotunan abubuwan da suka faru a zahiri ko kuma zane-zanen kwamfuta.
Ana iya nuna fim a gidan sinima, talabijin, wayar hannu ko kafafen kallon fina-finai ta intanet.
Misalan nau’o’in fim sun haɗa da:
– Fim ɗin soyayya.
– Fim ɗin tarihi.
– Fim ɗin yaƙi.
– Fim ɗin bincike (Documentary).
– Fim ɗin barkwanci.
2. MENENE WASAN KWAƘWAIYO?
Wasan kwaikwayo (Theatre/Stage Drama) wata fasaha ce da ake amfani da ita wajen gabatar da labari ko saƙo ta hanyar mutane masu taka rawa a gaban masu kallo.
A irin wannan wasa, jarumai kan fito a dandali ko wani wurin da aka tanada, suna magana, motsi da kwaikwayon halayen mutanen da suke wakilta.
Babban abin da ya bambanta wasan dandali shi ne ana gabatar da shi kai tsaye a gaban masu kallo, inda masu wasan da masu kallo suke kasancewa a wuri ɗaya a lokacin gabatarwar.
Misalai:
– Wasan kwaikwayo a gidan wasan kwaikwayo.
– Wasan kwaikwayo a makaranta.
– Wasan kwaikwayo a wurin taron al’umma.
Sai dai ana iya ɗaukar wasan kwaikwayo da kyamara domin a nuna shi a talabijin ko intanet. A wannan yanayin, an yi rikodin wasan ne domin mutane su iya kallonsa a wani lokaci ko wuri daban.
3. MENENE SHIRIN TALABIJIN?
Shirin talabijin (Television Programme) shi ne wani shiri da aka tsara domin gabatarwa ga masu kallo ta hanyar tashar talabijin.
Ba lallai ne duk shirin talabijin ya kasance fim ba. Akwai nau’o’i da dama, kamar:
– Labarai (News).
– Tattaunawa (Talk Show).
– Wasannin kwaikwayo.
– Shirye-shiryen ilimantarwa.
– Documentary.
– Wasannin motsa jiki.
– Shirye-shiryen nishaɗi.
Wasu shirye-shiryen talabijin ana ɗaukar su ne tun kafin lokacin watsawa, wasu kuma ana gabatar da su kai tsaye (Live).
4. MANYAN BAMBANCE-BAMBANCEN DA KE TSAKANINSU
Abu| Fim| Wasan dandali| Shirin talabijin
Manufa| Labari, ilimi ko nishaɗi| Gabatar da labari kai tsaye| Isar da shirye-shirye
Yadda ake samarwa| Ɗaukar hoto da tsara shi| Gabatarwa a gaban masu kallo| Ɗauka ko gabatarwa kai tsaye
Inda ake kallo| Sinima, waya, TV da intanet| Dandali ko gidan wasan kwaikwayo| Ta tashar talabijin
Nau’o’i| Soyayya, tarihi, Documentary| Drama, barkwanci da sauransu| Labarai, wasanni, tattaunawa da sauransu
5. SHIN FIM ZAI IYA ZAMA SHIRIN TALABIJIN?
Eh!
Fim na iya zama shirin da aka samar domin talabijin. Haka kuma ana iya nuna fim ɗin da aka shirya domin gidan sinima a talabijin.
Wannan yana nuna cewa fim yana bayyana nau’in aikin da aka samar, yayin da talabijin take bayyana hanyar watsa shirin ga jama’a.
Haka kuma, wasan kwaikwayo na iya zama wani ɓangare na fim. Saboda haka, ba daidai ba ne a ce duk abin da ake kira Drama dole ne a gabatar da shi a dandali.
6. ME YA SA YA KAMATA MU FAHIMCI BAMBANCIN?
Fahimtar waɗannan bambance-bambance zai taimaka wa masu shirya fina-finai, jarumai, ‘yan jarida da masu kallon fina-finai wajen gane nau’in aikin da suke gabatarwa.
Haka kuma zai taimaka wajen fahimtar yadda ake tsara shirye-shirye da kuma irin ƙwarewar da ake buƙata a kowane fanni.
KAMMALAWA
Fim, wasan kwaikwayo da shirin talabijin duk hanyoyi ne na sadarwa da nishaɗantarwa, amma suna da bambance-bambance a yadda ake samar da su da kuma yadda ake gabatar da su ga jama’a.
Fim aikin gani da sauti ne; wasan kwaikwayo na dandali yana dogara da gabatar da rawar kai tsaye a gaban masu kallo; yayin da talabijin take zama hanyar isar da nau’o’in shirye-shirye ga jama’a.
A FITOWA TA GABA:
SU WAYE DARAKTA, FURUƊUSA, MARUBUCIN LABARI DA JARUMIN FIM?
Za mu bayyana ayyukan waɗannan mutane da irin rawar da kowannensu yake takawa wajen samar da fim.
DUNIYAR FIM
Mu fahimci Fim kafin mu yi hukunci a kansa.
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
