Dole ne ku zama sojoji masu horo, ku zama sojoji masu aminci.
Alfijir Labarai ta rawaito Babban kwamandan runduna ta 81 ta Najeriya (NA), Manjo Janar Mohammed Takuti Usman, ya bukaci sojojin da ba zasu suyi biyayya ba ga Tinubu su ajiye aikin su.
Usman wanda ya yi kira da a yi biyayya ga shugaban kasa Bola Tinubu da hukumomin da aka kafa a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya kuma buƙaci sojoji da su kasance masu kwarewa tare da nuna cikakken biyayya tun daga shugaban kasa har zuwa babban matakin soja.
Yayin da yake jawabi ga sojoji a 35 Artillery Brigade, Alamala, Abeokuta, Jihar Ogun, Rundunar Sojojin Najeriya GOC ta lura cewa, akwai wasu kalubale.
Yayin da muke duba kalubalen da yadda za a magance su, dole ne ku zama sojoji masu horo, ku zama sojoji masu aminci.
Dole ne ku kasance masu aminci. Babu wani wuri ga sojojin da ba sa biyayya ga hukumar da aka kafa, Idan ba za ku kasance masu aminci ba, to, ku bar aijin ku tafi ku yi wasu ayyuka. amma ƙananun sojoji ba za su iya jurewa idan ba ku da aminci.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin juyin mulkin da sojoji suka ya fara zama ruwan dare a wasu kasashen Afirika inda Gabon ta kasance na baya-bayan nan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM