Dan Bello Katon Makaryacine Kuma Azzalumi – Amma fa In Ji Jibwis

IMG 20250331 161611

Na kalli Video da Dan Bello yayi yana zargin Sheikh Abdullahi Bala Lau da kungiyar Izala da karban kudi a hanun Gwamnatin tarayya da sunan gina ajujuwa, kuma yake cewa wai an cinye kudin ba’ayi aikin ba.

Abunda ya bani mamaki shine yanda tsananin son ɓata sunan Malamai ya rufewa Dan Bello ido ya gagara gane description na aikin gine-ginen ajujuwan da yake magana akai, wanda duk wanda yake da ilimi kuma ya sanya nutsuwa zai gane meye abun yake nufi cikin sauki.

Aiyyukan ginin ajujuwa da Dan Bello ya nuna, CONSTITUENCY PROJECTS na HON. MUKHTAR ALIYU BETARA, Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Bayo/Biu/Kwaya-Kusar… Federal Constituency a Majalisar Wakilai.

Yanda description na aikin yake shine, Hon. Mukhtar Betara ya saka zai gina ajujuwa wa kungiyar Izala da Sheikh Bala Lau yake jagoranci, wacce itace ake cewa “IZALA KADUNA”, haka nan zai gina ajujuwa a makarantun kungiyar Izala da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir yake jagoranci, wacce ita ake nufi a takaddar da cewa IZALA JOS, kuma zai ginawa yan Darika ma har bangarori biyu, dukka za’ayi wannan gini ne a Kwaya-Kusar LGA Borno State, kamar yanda yake jikin screenshot da nayi attaching a kasa.

Sunan JOS da KADUNA da akayi amfani dashi ba anyi ne don bambancewa tsakanin Izala 1&2, ba wai aiyyukan a JOS da KADUNA suke ba, kamar yanda shi Dan Bello ya fada.

Haka nan abunda Dan Bello ya saka na cewa an ware kudade domin ginin ajujuwa a JIBWIS Collage of Education Jega, Kebbi State, shima Constituency projects ne na Senator da yake wakiltar yankin a Majalisar dattijai, Senator Muhammad Adamu Aliero, kuma Senator Aliero shi ya gudanar da aikinsa da kansa, ba kungiyar Izala aka turawa kudi ba kamar yanda Dan Bello ya fada.

Shima wannan aikin daƙiƙi Dan Bello yace wai ba’ayi ba, kuma karya ne Senator yayi aikin kamar yanda yayi alkawari a wani taron kaddamar da Collage din (Akwai hoton allon kaddamar da ginin da Sunan Senator Aliero, da kuma hotunan makarantar a kasa).

Wallahi tallahi na jima da gane cewa abubuwa da yawa da Dan Bello yake fada shaci-faɗi ne kawai, yana samun karbuwa ne a wajen mutane kawai saboda yana attacking shugabanni ne, sakamakon rashin jituwa da take tsakanin talakawa da shugabanni.

Duk wanda yake son fahimtar gaskiya kan abunda na fada, ya nutsu ya sake kallon video Dan Bello with an open and objective mind.

Lalle Ɗan Bello ya tabka kuskure a wannan bincike da yace yayi, wanda ke ciki da sharri da cin mutunci ga shugaban mu, wannan kuma ya kara tabbatar mana da cewa akwai waɗanda suke ɗaukar nauyin sa da bashi bayanan ƙarya, domin biyan buƙatar kan su.

Da farko dai yace Sheikh Abdullahi Bala Lau Yana da akawun sunfi guda talatin, wannan ƙarya ne tsagworanta, zamu so ya kawo mana cikekken bayani akan waɗannan akawun guda talatin da ya faɗa ɗaya bayan ɗaya.

Duk waɗannan zarge-zarge da Ɗan Bello yayi basu da alaƙa da Sheikh Bala Lau ko ofishin sa a matakin ƙasa, kuma bai san da su ba.

A ƙusa da ƙarshe Ɗan Bello ya bada adireshin wani office a garin Lau dake jahar Taraba, wannan ƙarya ne, Sheikh Bala Lau bayi da wani office dake zama a Lau mallakar sa, in banda gidansa wanda in yaje garin yake sauƙa da iyalansa.

A ƙarshe Ɗan Bello ya ƙarƙare da cin mutuncin shugaban mu da ƙiransa da suna na ƙasƙanci.

Matsayar mu: Da farko dai mun kai ƙararsa wajen Allah, tare da addu’ar Allah ya nuna misali da shi, shi da dukkan masu aiki irin nasa, su girbi abun da suka shuka tun anan duniya.

Abu na biyu, zamu je kotu da shi domin yazo ya bada dukkan bayanan abun da ya faɗa, musamman yadda ya samo BVN tunda munsan ko hukuma ce zatayi bincike irin haka, sai ta nemi izini daga mahukunta, Insha Allah da Ɗan Bello da waɗanda suke temaka masa da labaran ƙarya ƙarshenku yazo, domin sai gaskiya ta bayyana Insha Allah.

Sannan akwai buƙatar Ɗan Bello yasan waye shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau a ɓangaren kasuwanci tun kafin ya zama shugaban JIBWIS, yafi ƙarfin waɗannan kuɗin da yake ambatawa.

Jibwis Nigeria

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *