Da Ɗumi Ɗuminsa: Wasu Ƴan Bindiga Sun Yi i Garkuwa Da Shugaban Jam’iyyar APC

‘Ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti Paul Omotosho.

Alfijir Labarai ta rawaito an tattaro cewa an yi garkuwa da Omotosho a kan hanyar Agbado-Imesi-Ekiti a karamar hukumar Gbonyin a jihar, da yammacin ranar Asabar.

Wata majiya ta kusa, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana cewa Omotosho wanda dan garin Imesi-Ekiti ne, yana kan hanyarsa ta zuwa garinsu ne a lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa motar sa kwanton bauna tare da harbe-harbe na wasu lokuta kafin su kai shi daji.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Segun Dipe, ya shaida wa DAILY POST cewa, “Eh, an yi garkuwa da shugabanmu da yammacin yau, kuma mun riga mun hada gwiwa da jami’an tsaro wajen ganin an sako shi.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *