Alfijr ta rawaito cewa Alasan Ado Doguwa na kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah, in da aka cafke shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano ranar Talata.
Kamen ba zai rasa nasaba da kisan da aka yi wa magoya bayan ‘yan adawa kusan 15 a karamar hukumar Tudun Wada a lokacin zaben da aka kammala ba.
Rahotanni sun ce an kulle wasu daga cikin mutanen da ba su da basu ji, basu gani ba a wani gini in da suka kone kurmus, lamarin da ya sa aka gagara ceto su.
Wasu da dama ne Doguwa ya harbe tare da jikkata shi a yunkurinsa na lashe zaben.
Bidiyon da jaridar SAHELIAN TIMES ta gani, sun nuna gawarwakin da aka kona daga ofishin NNPP na Tudunwada.
A daya daga cikin faifan bidiyon an yi hira da wanda aka kashe inda ya bayyana Doguwa a matsayin wanda ya harbe shi.
Alasan Ado Doguwa Ɗan Jamiyyar APC ne wanda ke da mukamin majority leader a majalisar Nijeriya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Wallahi rashin sanin makamar aikinku ya yi yawa, ba ku iya rubutu ba, rahotanninku cike suke da kurakuran rubutu, da abubuwa marasa ma’ana, mutum sai ya karanta rahoton ku ya rasa ina ne kan rahoton ina ne Gindin sa
Allah yakiyaye wannnn masifa allah yayi mana maganinta kasarmu najeria allah ya kawo mana zaman lpy