Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya mayar da makudan kudade har Naira Tiriliyan 4 a asusun gwamnatin tarayya da ya sace a lokacin da yake rike da mukamin shugaban babban bankin kasar.
Alfijir Labarai ta rawaito Wani mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan kuma mawallafin Point Blank News, Mista Jackson Ude ne ya bayyana hakan a shafinsa na “X” (Twitter), @jacksonpbn, ranar Talata.
A cewar majiyoyin da ke kusa da masu binciken, baya ga rahoton cewa ya mayar da Naira tiriliyan 4, Emefiele ya kuma yi watsi da mallakar wasu bankuna shida da ke da alaka da shi.
Hakazalika majiyar ta bayyana cewa, wani mataimakin gwamnan CBN Tunde Lemo, shi ma an ce ya mayar da kudaden masu biyan haraji da suka wawure dala miliyan 500.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Wani abin da ya fi ba da mamaki shi ne, an gano dala miliyan 275 a asusun ajiyar banki na wani dan Sabiu Yusuf mai shekaru shida, a.k.a Tunde, mai taimakawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman.
Haka kuma an gano wasu Naira tiriliyan 1.5 a cikin asusun tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Buhari.
Majiyar ta ce: “Mai bincike na musamman, Jim Osayande Obazee da kwamitinsa, ana zargin sun gano dala miliyan 275 a wani asusu a wani sabon banki na dan Sabiu Yusuf mai shekara shida a duniya
“Wasu Naira Tiriliyan 1.5 kuma ana zargin Yusuf, wanda ke da tasiri sosai a Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana tattaunawa a halin yanzu, yana amfani da wasu masu fada a ji a Najeriya kan yadda za a mayar da kudaden ba tare da fallasa su ba.
“Kwanan nan ne, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya koka kan yadda gwamnati mai ci ta gaji kasar cikin fatara daga gwamnatin Buhari saboda dimbin satar da aka yi a lokacin.”
News Band
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
Gaskiya shugaba Tinubu ya yi kokari, kuma mu na fatan ya ci gaba dakarbo kudaden dawasu su ka sace; har zuwa sanda za a biya bashin Nageria ko da ba duka ba.