Da Ɗumi-Ɗuminsa: Kotu Ta Kori Sanatan APC Kwanaki 46 Kafin Zaɓen 2023

Alfijr ta rawaito wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Adamawa ta kori Sanata Ishaku Abbo a matsayin dan takarar Sanatan Adamawa ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben bana.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da mai shari’a Mohammed Danladi ya yanke a ranar Talata, 10 ga watan Junairu, 2022.

Kotu ta kori Sanata Abbo bisa hujjar cewa unguwarsa da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa ta kore shi daga jam’iyyar.

Mai shari’a Danladi, ya bayyana cewa Sanata da APC na da nasaba da kudurin da majalisar zartarwar jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Mubi ta Arewa ta yanke na korar shi daga jam’iyyar a ranar 7 ga watan Oktoba 2022.

Kotun ta kuma yi watsi da cewa Sanata Abbo ba shi da hakki, don cin moriyar duk wani hakki ko wata gata da aka bai wa ’yan APC.

A ranar 7 ga watan Oktoban 2022 ne shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa ya amince da korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya bayar.

Kotun ta kuma hana jam’iyyar APC da Sanatan ke neman tazarce a karkashinta kar ta amince da shi a matsayin dan takararta, inda ta ce ba zai iya zama dan takarar jam’iyyar ba a zabe mai zuwa.

Hukuncin ya kuma hana Sen. Abbo bayyana kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar a yankin Sanatan Arewa a zabe mai zuwa.

Mai shari’a Danladi, ya ce lauyan wanda ya shigar da kara ya tabbatar da babu shakka kuma kotun ta gamsu da tsarin da jam’iyyar ta bi, inda ya ce an bai wa Sanata damar kare kansa amma da gangan ya ki yin hakan.

Ya ce matakin da masu shigar da kara suka yi na gurfanar da Sanatan ba wai na cikin gida ne na jam’iyyar ba kamar yadda suka yi ikirari, kuma suna da hurumin shigar da kara a kansa tunda su ‘yan jam’iyyar ne.

Idan dai za a iya tunawa, wasu ‘yan jam’iyyar APC guda biyu Abdullahi Suleiman da Yusha’u Usman na mazabar Kolere da Sabon Layi a karamar hukumar Mubi ta Arewa sun kai karar Sanatan tare da neman a yi masa tafsiri kan matsayin sa a APC.

A nasa martani, Lauyan wadanda suka shigar da kara, Abubakar Ali Esq, ya yaba wa kotun, inda ya ce hukuncin zai zama dakile kura-kurai na ‘ya’yan jam’iyyar da ke ikirarin sama da jam’iyyar.

Lauyan wanda ake kara, E. O. Odo, ya ce zai sanar da wanda ake tuhuman hukuncin da kotun ta yanke, inda ya ce idan ya amince za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *