
Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta wa direbobin baburan Adaidaita Sahu bin manyan Titinan jihar.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan yau Talata 29 ga watan Nuwamba wadda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA Nabilusu Abubakar Kofar Nai’sa ya fitar ga manema labarai
Sanarwar ta ta ce, Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa matuƙa Baburin Adaidaita Sahu bin manyan titinan daga gobe Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.
“Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan Adaidaita Sahun,” a cewar Sanarwar.
Titinan da aka haramtawa direbobin baburan Adaidaita Sahun sun hada da titinan Amadu Bello zuwa mahaɗar Munduɓawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, Gwamnatin jihar Kano za ta sanar da ranar da direbobin Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c