
Alfijr ta rawaito Gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ya bayar da wannan umarni a taron kwamitin bankunan da aka gudanar a ranar Lahadi, 12 ga Maris, 2023.

A cewar umarnin, masu ba da lamuni a bankunan kasuwanci su samar da lambobin ajiyar kudi kuma babu iyaka ga adadin na lokuta mutum ko kamfani na iya yin ajiya.

Da yake tabbatar da ci gaban a safiyar Litinin, 13 ga Maris, 2023, gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya ce; “Emefiele da kan sa ya tabbatar min da abin da ke sama a yayin tattaunawa ta wayar tarho a daren Lahadi”.
Gwamnan ya bukaci mazauna jihar Anambra da su karbe tare da yin mu’amala da tsofaffin takardun kudi (N200; N500; da N1,000) da kuma sabbin takardun kudi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
I really appreciate your good workings and so also recommended it to the general public. May Allah Ta’ala uplift your Status co. Ameen