Alfijr
Alfijr ta rawaito wasu‘yan bindigan sun kai wa tawagar shugaban kasa farmaki ne a yayin zuwan shugaba Buhari garin Daura domin hutun sallah.
Jami’an tsaron tawagar gaba mai sharar hanyar zuwan shugaba Muhammadu Buhari Daura domin bikin Sallar Idi tayi nasarar karya lagon harin da yan ta’adda suka kaiwa Jerin Gwanon motocin na shugaban kasa:
Alfijr
Wannan harin dai ya faru ne a kusa da garin Dutsin-Ma yayin da tawagar ta shugaban kasa mai ɗauke da jami’an sharar fage da yan jaridu ke kan hanyarsu ta zuwa Daura kafin isowar shugaban kasa domin halartar bikin babban sallah da zai gudana ranar asabar mai zuwa.
Yan ta’addan sunyi kwanton-bauna ne domin kai harin, yayin jami’an soji da yan sanda da SS dake cikin tawagar suka maida martani mai zafi inda suka tarwatsa Yan ta’addan baki daya.
Alfijr
Yanzu haka mutum biyu dake cikin tawagar ta shugaban kasa suna kwance a wani asibiti suna karbar magani domin wasu raunuka da suka samu a yayin harin.
Tuni sauran jami’an dake cikin tawagar suka isa garin Daura domin jiran isowar shugaban kasa.
Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da wannan hari.