Rundunar Ƴansanda ta jihar Kano ta sanya ladan Naira dubu 100 ga duk wanda ya kamo ko samar da bayani da ya kai ga kamo daya daga cikin wasu fitinannun ƴan daba guda uku da ta ke nema ruwa a kallo a jihar.
Alfijir Labarai ta rawaito Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wajen buɗe gasar ƙwallon ƙafa tsakanin rundunar da wasu tubabbun ƴan daba a jihar, wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba.
Kwamishinan ya bada sunayen ƴan daban da suka haɗa da
Abba Burakita da ke Unguwar Dorayi,
Cile Maidoki da ke Tudun Fulani
Hantar Daba da ke unguwar Kwanar Diso,
Dukkanninsu a kwaryar birnin jihar.
A cewar Kwamishinan, shi zai bada ladan a aljihunsa, inda ya ce matasan sun adabi al’umma yankin su kuma an nemi su tuba sun ƙiya.

Ya kara da cewa a kwanan nan rundunar ta gayyaci wasu ƴan daba guda talatin domin tattauna wa da su kan yadda za su tuba a kuma taimaka wa rayuwar su, ya kara da cewa “a maimakon talatin din nan, sai da muka samu guda casa’in sun kawo kan su.”
“A cikin waɗanda muka gayyata har da guda ukun nan da muke nema saboda su sun ki su amsa gayyatar ta mu.
Don haka muna neman su ruwa a jallo, son haka wanda ya kamo ko ya ba da wani bayani muhimmi da zai kai ga an kamo su, zan bashi Naira dubu 100 idan ma duka ukun ne, dubu 300 kenan kuma a aljihu na zan bayar,” in ji shi
Ya ce an hada wasan ne domin wani salo na yaƙi da dabanci ta hanya mai sauki domin sanya su ƴandaban su ji cewa ana kaunar su a cikin al’umma.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI