Bikin Sallah: Buhari Ya Bada Kyautar Saniya Da Shinkafa Buhu 10

IMG 20240616 WA0207

Daga Aminu Bala Madobi

Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada mahimmancin dogaro da kai wajen samar da abinci.

Alfijir labarai ta rawaito da yake jawabi bayan halartar Sallar Idi tare da Sarkin Daura, Alh. Faruk Umar Faruk, Buhari ya yaba da kokarin ‘yan Najeriya da suka yi na komawa harkar noma domin rage tsadar kayan abinci da kuma samar da wadataccen abinci a kasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar.

A cikin sanarwar, ya yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da kokarin dogaro da kai ta hanyar noma da cin abincin da ake nomawa a cikin gida.

Ya ce, “Ina yiwa kowa barka da Sallah. Wannan biki na musamman ya kawo mana farin ciki, wadata, da lafiya mai ban sha’awa ga kowa.

Wannan ba lokacine da za mu ja da baya bane, lokacine da muka ga farashin yana ta tashi, don haka mu sayi abin da ake nomawa a kasar.”

Tsohon shugaban kasar ya bayyana irin ayyukan da gwamnatocin baya suka yi wajen samar da kasa mai inganci da kwanciyar hankali, inda ya bukaci matasa da su himmatu wajen gina kasa da kuma samun kwarin guiwa daga iyayen da suka kafa kasar da kuma shugabannin yankin.

Yayin da ya ke yin tsokaci kan manyan tarukan da aka yi a wajen bukukuwan Sallah, Buhari ya nuna damuwarsa kan karuwar al’umma da ba a kula da su, inda ya yi gargadin cewa hakan ka iya haifar da gagarumin kalubale a nan gaba.

“Akwai bukatar kara tattaunawa da wayar da kan jama’a game da wannan matsala, da kuma bukatar kara saka hannun jari a fannin ilimi da lafiya,” in ji shi.

Sai dai ya ja kunnen ‘yan Najeriya da su rika tallafa wa juna a wadannan lokutan, inda ya ce, “Idan aka yi la’akari da halin da kasar ke ciki, da kuma yadda ake gudanar da bukukuwan Sallah, mu taimaki juna, mu zama masu rike da ‘yan uwanmu. Ina yiwa kowa barka da Sallah.”

Da yake jawabi ga mambobin kungiyar matasa masu yi wa kasa hidima, wadanda suka ziyarce shi a wani bangare na al’adarsu ta Sallah, ya yaba wa hukumar NYSC a matsayin muhimmiyar rundunar hadin kan Najeriya.

Ya yaba da shirin a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da Janar Yakubu Gowon ya samu tare da yin kira ga gwamnatocin da za su ci gaba da karfafa shi, yayin ziyarar Buhari ya basu kyautar saniya da buhun shinkafa 10 domin shagulgulan sallah

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *