Badakalar Kudi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukunta Faisal Abdurrashid Maina

Alfijr ta rawaito Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta amince da hukuncin da aka yanke wa Faisal Maina, dan gidan tsohon shugaban rusasshiyar hukumar fansho ta PRTT, Abdulrasheed Maina, wanda ya gurfana gaban kotu.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC a kan tuhumar da ake masa na hada baki da kuma karkatar da kudade.

Kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, a wani hukunci daya yanke a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2022, ya yanke hukuncin cewa mai shari’a Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya samu Faisal da laifi.

Kotun ta ce EFCC ta yi nasarar tabbatar da cewa Faisal, yana gudanar da wani asusun banki na bogi a bankin United Bank for Africa, UBA, inda mahaifinsa Maina ya karkatar da zunzurutun kudi har naira miliyan 58.1.

Kotun daukaka kara ta lura cewa asusun da aka saka a cikin asusun ajiyar da aka yi amfani da shi da sunan Alhaji Faisal Farm 2, Faisal da mahaifinsa suka cire shi daga watan Oktoba 2013 zuwa Yuni 2019.

Mai shari’a Abang wanda a watan Oktoba 2021, ya samu Faisal. Wanda ake tuhuma a kan tuhume-tuhume uku na halasta kudaden haramun, ya ce ya gamsu da cewa hukumar EFCC ta tabbatar da duk wasu muhimman abubuwan da ke tattare da tuhumar, yana mai jaddada cewa wanda ake tuhumar ya kamata ya sani cewa kutsawa cikin asusun bankin ya samo asali ne daga wani haramtaccen aiki na cin hanci da rashawar mahaifinsa.

Kotun ta bayar da umarnin a rufe kamfanin da aka wawure asusun, Alhaji Faisal Farm 2, tare da mika wa gwamnati kudaden da ke cikinsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *