Amaryar mahaddaciyar Alqur’ani ce, kuma ga dukkanin alamu sun tabbata amarya tana aiki da abibda ta koya na fadin Allah ba kamar wadansu ba.

Alfijir Labarai ta rawaito a yayin gudanar da bikin auren babbar yar Fitaccen marubucin nan, kuma jarimi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, wanda ke taka rawar Gwamnan garin Alfawa na shirin kwana 90 a tashar AREWA24 Ado Ahmad Gidan Dabino MON, an sha farin ciki da sam barka a ranar 2 ga watan Satumba 2023
Wannan aure na Fatima Ado Ahmad da Angonta Bello Umar Kawaji ya kayatar da dukkanin jama’ar da suka halarce shi, musamman yadda aka ga amarya ta gayyato kawayenta suka sauke Alqur’ani mai girma don samun albarkar auren.

Lamarin ya faru ne a wani yanayin mai ban sha’awa, wato yayin hidimar bikin babu raye-raye da kade-kade da juye-juye, ha kuma babu kidan Djee balle a samu damar manne-manne tsakanin maza da mata da bisa al ada ake yi kofar gidan su amarya.
Amaryar mahaddaciyar Alqur’ani ce, kuma ga dukkanin alamu sun tabbata amarya tana aiki da abibda ta koya na fadin Allah ba kamar wadansu ba.
Muna adduar Allah yasa sauran y’an mata da samari da ba su yi aure ba, za su yi koyi da wannan aure, Allah Ya sanya albarkarsa, Ya sa mutuwa ce kadai za ta raba shi ameen.
Alfijir Labarai tayi kewayen kuturunka nawa ganin yadda manyan kasar nan suka suma halartar wannan aure mai tarihi, yayin kewayen mun ci karo da :-
- Mai girma Gwamnan Jigawa Mallam. Umar Namadi DAN-MODI FCA
- Rt. Hon. Haruna Aliyu DANGYATIN QS – Speaker Jigawa State House Of Assembly
- Rt. Hon. Sani Isyaku GUMEL – Deputy Speaker Jigawa State House Of Assembly
- Hon. Auwalu Danladi SANKARA – Commissioner Special Duties, Jigawa State
- Aminu Ahmad KANTA – Commissioner Commerce, Jigawa State.
- Hakimin Sankara Bunun Ringim, Sanusi Amadu.
Da kuma manya manyan jarumai daga masana antar Kannywood da ma aikatan tashar Arewa24, da sauran yan kasuwa da sarakai da malamai da ba zamu iya wallafa sunayensu ba.
Allah ya bada zaman lafiya da arziki mai daurewa ameen.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
I really like this media of alfijir as they bringing real news not pace.
Muna godiya
Allah sa albarka. Wannan abin koyi ne, kuma qalu-bale ne ga dukkan alummar Musulmi. (May Allah bless this union. This truly exemplary and indeed a challenge to the entire Ummah. Let’s see how we will go in moving this positive trend forward.)