‘
Ƙungiyar Dillalan Fetur Da Iskar Gas Ta Arewacin Najeriya, Ta Sha Alwashin Haɗa Hannu Da Kamfanin NNPCL Da Masu zuba Jari Na Ƙasashen Waje A Fannin Iskar Gas.
Alfijir Labarai ta rawaito yan Najeriya musamman ’yan Arewa na shirin ganin canji ta fuskar makamashi makam daga man Fetur da ake kira da PMS, zuwa yin amfani da Iskar Gas CNG, a daidai lokacin da ƙungiyar dillalan man Fetur da iskar Gas ta Arewa, AROGMA, ke shirin gayyato kamfanonin ƙasashen waje don saka hannun jari a harkar fannin na harkokin cinikayya tare da bunƙasa amfani da iskar gas a yankin.
Sabon zaɓaɓɓen shugaban kungiyar ta dillalan Fetur da Iskar Gas ta yankin Arewa AROGMA, Bashir Ahmad Dan-Mallam ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.
A cewar Dan-Mallam, AROGMA, tare da haɗin gwiwar Kamfanin Mai na Najeriya NNPCL, na shirin gayyato kamfanoni daga ƙasashen Qatar da Turkiyya da Jamus da kuma India domin samar da iskar gas a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa, AROGMA ta riga ta tuntuɓi abokan hulɗar su na ƙasashen ƙetare kuma tana nazarin shawarwarin su daban-daban.
Shugaban ya yi nuni da cewa, aikin zai zama babbar nasara ga Najeriya, kuma zai zama wani muhimmin ci gaban kasar nan musamman yankin Arewa.
Ya ƙara da cewa hakan zai sauƙaƙa wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke fama da shi musamman a Arewacin Najeriya, sakamakon cire tallafin man Fetur.
Dan-Mallam ya kuma yabawa wa ƙoƙarin da mahukuntan na NNPCL suke yi bisa goyon baya da jajircewa da suke bai wa mu ƴan kasuwa wajen saka hannun jari a wasu tsare-tsare na canja yin amfani da man Fetur, ɗin zuwa Gas da amfani da CNG da aikin gyaran matatun mai da dai sauransu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM