Alfijr ta rawaito Yan Majalisar Tarayya Masu Ci Guda Uku Na Jihar Katsina Sun bar Jam’iyyar APC sun koma Jam’iyyar PDP a jiya 29-01-2023.
Sun Bayyana Ficewar tasu ne bayan sun gana da Dan takarar Shugaban Kasar Nigeria na PDP a Jihar Sokoto.
Hakan na zuwa ne karkashin jagorancin tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina wanda shima ya watsar da Jam’iyyar APC a kwanakin baya, shine ya hada su da Atiku Abubakar din a jihar Sokoto.
Daga Cikin su yan majalisar sun hada da
- Hon Ahmed Dayyabu Safana (Dan Majalissar tarayya mai wakiltar Safana/Danmusa/Batsari Constituency)
- Hon Hamza Dalhat Batagarawa (Dan majalissar tarayya mai wakiltar Batagarawa/Rimi/Charanci Constituency)
- Hon Salisu Iro Isansi (Dan majalissar tarayya mai wakiltar Karamar hukumar Katsina Central Constituency).
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇