Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke zaɓen ’yan Majalisar Dokokin Jihar Plateau na jam’iyyar PDP su 11, sannan ta ayyana ’yan APC a kamar yadda halastattun suka lashe lashe kujerun.
Alfijir Labarai ta rawaito a hukuncin da suka yanke ranar Juma’a, alkalan da ke shaida ikon Mai Shari’a Okon Abang, sun ce duk kuri’un da dakatattun ‘yan majalisar suka samu a zabensu na watan Maris lalatattu ne saboda jam’iyyarsu. ba ta da shugabanci.
Alkalin ya ce PDP ta yi wa tanade-tanaden sashe na 177 na kundin tsarin mulkin Najeriya karan-tsaye, don haka ba ta samu ta fafata da ’yan takara ba a zaɓen.
Daga nan ne kotun ta ayyana dukkan abubuwan suka zo na biyu a zaɓen a kamar yadda suka lashe shi.
Yan majalisar da aka sami dai sun haɗa da; Hon Timothy Dantong (Riyom), Hon. Rimyat Nanbol,- (Langtang ta Arewa ta Tsakiya), Moses Sule (Mikang), Salome Waklek, (Pankshin), Hon. Bala Fwangji (Mangu ta Kudu), Hon. Maren Ishaku (Bokkos), Hon. Dagogot (Quaanpan ta Arewa) da Nannim Langyi,-(Langtang ta Arewa).
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Sauran sun haɗa da Nimchak Rims (Langtang ta Kudu) Hon. Danjuma Azi (Jos ta Arewa maso Yamma) Gwottson Fom (Jos ta Kudu) da Hon. Abubakar Sani Idris (Mangu ta Arewa).
Sakamakon wannan binciken, yanzu jam’iyyar ta APC ce ta koma mai girma a majalisar Jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp