Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun bayyana cewa marigayin ya bar wasiyya tun raye cewa a binne shi ne a birnin Madina a kasar Saudiyya idan ya rasu.
Wannan bayani ya fito ne daga Hajiya Amina Umar Fulani, daya daga cikin iyalan gidan, wadda kuma ’yar uwa ce ga marigayiya Hajiya Rabi Tajo Dantata, matar Alhaji Aminu Dantata da ta rasu a Madina shekaru biyu da suka gabata.
A cewarta, marigayin ya bayyana wannan wasiyya ce bayan rasuwar matarsa, inda ya bukaci da a binne shi a kusa da ita a Madina.
Tun da safiyar yau ne Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da shirin gudanar da sallar Ga’ib ga marigayin a masallacin Aliyu Bn Abi Dalib da ke Dangi a birnin Kano, da misalin karfe 2:00 na rana.
An tabbatar da cewa ya rasu ne a Dubai, kuma daga can ne za a dauki gawarsa zuwa Madina don cika wasiyyarsa ta karshe.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD