
Alfijr ta rawaito Sakataren Alhaji Aminu Dantata, mai suna Mustapha Abdullahi Junaid, ya musanta labarin da ake yaɗawa musamman a kafafen sada zumunta, cewa Dantata ya goyi bayan wani ɗan takarar kujerar gwamna a jihar Kano.

A ƙarshen makon jiya ne aka samu jita-jitar cewa, Alh Aminu ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, kafin daga bisani a gano cewa babu ƙamshin gaskiya a cikin labarin.

“Ina sanar da mutane cewa Alh Aminu Alhassan Dantata bai ce a zaɓi Gawuna ba, kuma bai ce a zaɓi kowa ba, domin shi Uba ne a wajen kowa, saboda haka masu yaɗa wannan jita-jita su daina kuma suyi gaggawa wajen cire post ɗin da sukayi. Mungode.
Mustapha A. Junaid
Secretary to Aminu Alhassan Dantata

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ