Akalla Mutane 20 Sun Mutu Yayin Da Cutar sankarau Ta Barke A Jigawa

Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Jigawa ta ce fiye da mutum 20 ne ake fargabar sun mutu sanadin cutar sanƙarau da ta ɓulla bana a jihar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta bayar da rahoto a makon jiya cewa mutum 18 sun mutu sanadin cutar ta sanƙarau da ta ɓarke a can.

Hukumomi a jihar Jigawa sun ce tuni suka gudanar da taron gaggawa da Hukumar Daƙile Cutuka ta Najeriya wadda ta yi alƙawarin aika riga-kafi ga mazauna yankunan kan iyaka.

Dr. Salisu Mu’azu, Babban Sakataren a ma’aikatar lafiya ta Jigawa ya yi karin haske kan cutar, Ita dai cutar sankarau cuta ce wadda take da hadarin gaske da take shafar kwakwalwa sannu  laka, kuma ta kasance babban jkalubale ga duniya .

Kwayoyin baktiriya su ne suka fi haddasa ta.
BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *