A Kalla Mutum 8 Sun Mutu Bayan Da Ƴan Fashi Suka Kai Wa Bankuna 4 A Najeriya

Screenshot 20221010 000910 com.facebook.katana edit 30872921640601

Tsautsayin ya rutsa da bankuna hudu da suka hada da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.

Alfijir Labarai ta rawaito akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan fashi da makami suka kai hari kan wasu bankuna a yankin Otukpo da ke Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa tsautsayin ya rutsa da bankuna hudu da suka hada da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.

Cikin wadanda suka rasa rai akwai ’yan sanda 3, dan sintiri daya, wani kansila a yankin da kuma masu hulda da banki guda biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa sai da barayin suka kai farmaki kan ofishin ‘yan sanda da ke daura da bankunan kafin samun damar aukawa cikin bankunan.

Akalla sun shafe sa’a daya suna sata kafin ficewa daga yankin suna harbin iska a motocin Hilux biyu da wata karamar mota daya.

Kakakin rundunar ’yan sanda, SP Catherine Anene ta tabbatar da aukuwar al’amarin, sai dai ta ce ba ta da cikakken bayani a kai

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *