Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Mabiya Shi’a 19 Da Suka Yi Zanga-Zanga A Abuja

Alfijr ta rawaito Jami’an sanda sun kama wasu mabiya kungiyar Shi’a (IMN) 19 da laifin kawo cikas da tayar da tarzoma, da kuma jerin gwano ba bisa ka’ida ba a Abuja.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan sakin shugaban kungiyar, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa, Zeenah ba tare da basu fasfo ɗin su na kasa da kasa ba.

Sama da mambobin kungiyar 400 ne suka gudanar da zanga-zanga daga babbar kotun tarayya zuwa dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Sun toshe hanyoyin, wanda hakan ya batawa jama’a rai, musamman matafiya, kuma sun bukaci a gaggauta sakin fasfo din shugaban nasu.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, Sufetan ‘yan sanda (SP) ya fitar a daren jiya ta ce, an tarwatsa haramtacciyar muzaharar ne, yayin da aka kama mutane 19 da ake zargi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *