
Alfijr ta rawaito BRICS na nufin Brazil, Rasha, India, China da South Africa.
Wannan wata kungiya ce da wadannan kasashe suka kafa a shekarun baya domin kare kansu daga danniyar da Amurka ke yiwa siyasar duniya.

A yanzu haka wannan kungiya ta na samun tagomashi daga sauran kasashen duniya irin su Saudi, Iran, Nigeria da Korea.
Idan wannan kungiya ta samu karfuwa a duniya to lallai karshen Amurka yazo.
Dama haka duniya take, haka Allah ya shirya juya mulki daga wannan zuwa wancan daula.
Babban motsin da wannan kungiya tayi na baya bayan nan shine yadda kasar Russia ta daina amfani da Dollar wajen sayar da Gas din ta.
Wato ta yi hukuncin cewa duk mai son hajar ta to sai ya biya ta da kudin kasarta wato Rubbel.
Wannan ya ragewa Dollar karfi matuka.

Daga baya Kasan Sin itama ta biyo baya, haka kuma zaá cigaba, wato kowace kasar da ke cikin wannan kungiya darajar albarkatun kasar ta shi ke nuna karfin tattalin arzikin ta.
Idan wannan abu ya tabbata lallai kasar mu Nigeria zata amfana matuka da arziki zai yalwata. Talauci zai ragu, za a samu cigaba cikin sauri.
Wani abu kuma da wannan kungiya tayi shine kokarin samar da fahimtar juna tsakanin Saudiya da Iran, kasashen da suka kwashe shekaru daruruwa suna gaba da juna.
Koda yake bambamcin akida ne tushen fadan su, amma hakan ya mamaye duk huldodin su na siyasa da zamantakewa, kuma ya haifar da yake-yake da rasa rayuwa masu yawan gaske.
Idan wannan zaman lafiya ya tabbata to shikenan zamu daina jin fadan Hisbullah da na Yan talban da ISIS kai har ma da Boko Haram domin duk suna da alaka da Juna.
Kasar China da Russia basu da manufa ta hada fada tsakanin kasashe, kawai don su kwashi arzikin kasar sabanin Amurka wacce kullum ta ke hada fada ta koma gefe tana sayar da makamai ga kasashen.
Tun a shekarun baya wani farfesan Amurka kuma masanin siyasar duniya mai suna Professor Jeffrey Sachs, ya gayawa shugabannin Amurkan cewa idan basu yi da gaske ba china fa zata kwace ikon siyasa da tattalin arziki daga hannun su.

A yau wannan magana ta fara tabbata, China tana shiga kasashe tana sulhun ta tsakanin su.
Babban abin lura anan shine mu a Nigeria ta yaya wannan cigaban siyasar duniya zai amfane mu?
Yaya zamu ci moriyar dimbin arzikin da muke dashi a kasarmu?
Yaya zamu kaucewa shiga wani sabon ramin na mulkin mallaka?
Yaya zamu sanya kasarmu akan turba mai dorewa don amfanin bayanmu?
Yaya zamu kaucewa barazanar da Amurka zata iya kawo mana a wannan cigaba?
Ina kira da babbar murya ga shugabanni, yan siyasa, malaman jami’a, yan kasuwa, sarakuna, yan siyasa, yan boko da duk yan Nigeria da mu farka mu fahimci inda duniya ta sa gaba a halin yanzu.
Alamu suna nuna cewa fa za a canjawa gyambo kafa.
A daidai lokacin da muke neman kusanci da Allah to kada mu manta rabon mu na duniya.
Allah ya taimake mu
MS Yunusa Esq. MICSAN, MNIArb
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ