Mata Sun Yi Barazanar Tafiya Tsirara A Abuja Kan Sakamakon Zaɓe

Alfijr ta rawaito Wasu fusatattun mata, a karkashin kungiyar ‘Angry Nigerian Women’ a yau Talata sun mamaye babban titin da ke kan hanyar zuwa babban dakin taro na kasa da kasa, wurin da ake tattara wa da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, bisa zargin tafka magudi.

The Punch ta wallafa cewa matan sun kuma yi barazanar za su tafi tsirara, idan har hukumar zabe mai zaman kanta ta ki amincewa da bukatarsu kan dalilin da ya sa ba a aika sakamakon zaben shugaban kasa ta hanyar yanar gizo zuwa babban dakin tattara sakamakon zaɓe na INEC yadda kowa zai gani.

Matan da ke rera wakoki irin su ‘ba mu yarda ba’, ‘Mahmood ya nuna mana sakamako’, ‘asali sakamakon da muke so’ suma suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce daban-daban da suka hada da, ‘INEC ki dena magudi’, ‘makomar ‘ya’yan mu muke ji, ‘Mahmood ka bamu sakamakonmu’, ‘mun gaji da zalunci’ da sauran su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *