Kowa Ya Kwana Lafiya: Sakon Ga Ƴan Najeriya Kan Zaman Lafiya

Daga Kamaluddeen Ahmad

A yayin da Najeriya, kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, kasa ta bakwai mafi yawan al’umma a duniya, mai dauke da mutane sama da miliyan 200, kuma kasa ce mai kabilu daban-daban mai harsuna sama da 520, da ke shirin gudanar da zaben shekara na 2023, manufar majalisan Dinkin duniya na ci gaban al’umma mai dorewa mai lamba 16.

Waton zaman lafiya da adalci da cibiyoyi masu kwazo da hazaka, ya rataya ne a kan shugabanni, da hukumar zabe, da hukumomin tsaro, da ‘yan siyasa, da kuma bangaren shari’a,
da masu kada kuri’a da matasa, don gudanar da sahihin zabe mai inganci, wanda zai tabbatar da tsaro na siyasa a Nijeriya.

Ya kamata ‘yan siyasa su yi koyi da tsohon shugaban kasa, mai girma Dokta Goodluck Ebele Jonathan, wanda ya ce: “Burinsa na kashin kansa bai cancanci zubar da jinin dan Najeriya ba.”

Daga tashin hankalin da ke da nasaba da zabe zuwa rigingimu da makami, matasa ne suka fi yawa a cikin.

Kuma a Yawancin rikice rikicen tashin hankali da ke faruwa a fadin duniya, Yara, da mata, da tsofaffi, su suka Fi cutuwa.

Kamar dai yadda ya faru a Libya, Syria, Yemen, Ukraine da sauran kasashe da ke fama da yaki, rikici ya kan bar baya da kura da suka hada da yunwa da rashin abinci Mai Gina jiki, cututtuka saboda rashin tsaftatancen ruwan Sha da kiwon lafiya, tabarbarewar ilimi da ababen more rayuwa, Kai hatta da gurbacewar muhalli, Mai haifar da sauyin yanayi ko dumaman yanayi, Wanda ke Kara yin barazana ga rayuwar Dan Adam a Doron kasa.

Nijeriya ita ce kasa daya tilo da muke da ita! Shekaru sama da 60 mu ka kwashe kafin mu kasance inda muke yau.

Dole ne mu kasance masu juriya da bin doka da oda, mu yi watsi da duk wani nau’in daba na siyasa da zai kawo cikas wajen kada kuri’a, sannan mu guji tashin hankali bayan an bayyana sakamakon zaben.

Kudirin Majalisar Dinkin Duniya kan matasa, zaman lafiya, da tsaro ya amince da rawar da matasa ke takawa wajen magancewa da hana rikice-rikice, ya kuma bukaci karin wakilcin matasa wajen yin shawara a dukkan matakai.

Nagode!

Kamaluddeen Ahmad
Mai Rajin Yada Manufofin Majalisar Dinkin Duniya Na cigaban Al’umma Mai Dorewa (SDGs).

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *